A 'yan kwanakin nan kasuwar 'yan zamba na yanar gizo ta bude inda kullum suke kawo wata hanya domin damfarar wadanda basu gama wayewa da harkokin INTANET din ba. Wasu lokutan zaka ga an turo maka link na wani tallafi da sunan wani shahararren mutum ko kuma kungiya ko kamfani, ko kuma ace za'a baka tallafin karatu ko aiki mai albashi mai tsoka. Mafi yawancin wadannan abubuwa dai na yaudara ne duk da ana samun wadanda suke na gaske, to amma insha Allah a cikin wannan rubutun zamu sanar daku hanyar da zaku ringa bi wajen tantance sahihancin duk wani tallafi da aka ce za'a bayar.
Ga kadan daga cikin hanyoyin da ake gane shafukan yan damfarar INTANET nan 👇👇👇
1. Duk shafin da yake tallata wani tallafi da sunan wani shahararren mutum ko kamfani ko kuma kungiya, sai a cikin sharadin samun tallai aka ce sai ka turawa wani, to 'yan damfara ne. Ana gane sahihancin labarin ne ta hanyar ziyartar shafin soshiyal Midiya din mutumin, kamar Facebook ko Twitter. A kula: Duk shafin shahararren mutum a Facebook ko Twitter yana da alama ruwan bila a gaban sa, hakan ne yake tabbatar da cewa nashi ne. Idan ka ziyarci shafin nashi sai ka duba ko akwai wani labari mai alaka da wanda aka turo maka, idan babu kawai kayi watsi da wanda ka gani.
2. Idan ka je cike wani tallafi aka ce ka bada bayanan ka na banki bayan Account Number da Account Name, to da yiwuwar idan ka bayar a cire maka kudi da wannan bayanan. Ka guji bayar da PIN din ka na ATM ko na Mobile App. Kada ka sake ka dauki hoton ATM din ka ka turawa wani, koda kuwa babu komai a ciki. Lambobin CVV, MM/YY, da CARD NUMBER suna da tsaro, kada ka bayyanawa wanda baka sani ba ko wanda kaga alamun ya waye da harkar INTANET.
3.Mafi yawancin masu ikirarin cewa zasu bada tallafi indai suna amfani da URL SHORTENER to ba na gaskiya bane, shafin bada tallafi na gaskiya yana zaune ne a URL mai irin sunan wadanda zasu bada tallafin.
4. Idan ka je cike irin wannan tallafin sai kaga an baka bankunan da zaka iya saka account number din ka kala biyu ko daya kacal, to kada ka saka saboda watakila suna ganin saukin yin damfara ne ta bankunan da suka saka.
Idan gwamnati ce zata bada tallafi zaku ga shafin da za'a bayar da tallafin ya kare da .gov.ng, idan baku ga haka ba, to ba lallai ya zamo na gaskiya ba.
Domin neman karin bayani akan abubuwan da suka shafi INTANET da almundahana a INTANET din, ko kuma yadda ake dawo da kudin da masu yin damfarar suka sace daga banki, zaku iya tuntubar mu ta nambar waya 👇👇👇
08116234604
.jpeg)
.jpeg)
0 Comments