ILLOLIN YIN BLEACHING GA DAN ADAM

BLEACHING (Bilitin) wata hanya ce da ake bi wajen sauya launin halittar fata zuwa fara ko kuma mai haske.

Mafi yawancin masu yin bleaching dai mata ne, inda a wani bangaren ake samun maza wadanda su ma suke yin bleaching din.

Illar yin bleaching


Da yawan masu yin bleaching (Bilitin) basu san illar da take tattare da yin Bilitin din ba, hakan ne yasa suke kai kan su mahallaka ba tare da sun ankara ba.


A mafi yawancin lokuta masu bleaching sun fi yin amfani da maya-mayai domin yin hakan, wasu kuma suna amfani da allura domin rikida launin fatar tasu zuwa fara. A wasu lokutan ma ana iya samun masu zuwa ayi musu tiyata (surgical surgery) domin sauya launin fatar tasu.

Illar yin bleaching


To amma shin ko wadanda suke yin bleaching din sun san allar yin shi?


Ga kadan daga cikin ILLOLIN YIN BLEACHING din 👇👇👇

Illar yin bleaching


  1. Yana jawo fushin Allah ga mai yi.
  2. Idan mai yi ya mutum bai tuba ba Allah zai kama shi da laifin raina halittar da Yayi masa tare da sauya ta.
  3. Yin bleaching yana nuna cewa kana nunawa Allah yadda ya kamata Ya yi ka😭

  1.  Idan mutum ya dade yana yi, sannan ya daina, yana zama kamar wani dodo saboda muni. 😢
  2. fatar mutum tana rage karko sanadiyyar rasa wasu sinadarai.
  3. wani hasken fatarsa zai yi yawa ta yarda har kalar jijiyon jikinsa zaka iya gani.
  4. Jikin mutum ya dinga wari ta yarda da ka matso kusa dashi zaka dinga jin wani wari Mai kama da karnin kifi.
  5. Idan bleaching yayi yawa yana taba koda (kidney failure).
  6. Yana kawo cutar daji (skin cancer)
  7. Yana sa raunin karfin fata 
  8.  Mace me ciki kuma yana kawo lalacewar Dantayin cikinta
  9. kawo juyayin mahaifa
  10. Yana rage Kaurin fata
  11. Yana sa zubar jini Sosai In mutun Yaji ciwo.. 😭
Allah yasa mu dace.