Da yiwuwar Messi dan wasan Paris Saint Germain (PSG) kuma tsohon dan wasan Barcelona ya koma taka leda a Barcelona.

Messi din wanda yafi kowanne dan wasa yawan samun kyautar Ballon D'Or inda ya sami guda 7, ya bar Barcelona ne a shekarar 2021 sannan ya koma PSG saboda matsin tattalin arziki da Barcelona ta tsinci kan ta a wancan lokacin.

Lionel Messi


To saidai a wata hira da aka yi da  Jordi Cruyff, Darakta a Barcelona yace da yiwuwar Messi ya sake dawowa Barcelona amma bai fadi lokacin dawowar tashi ba. Amma a maganar shi kamar Messi din ba lallai ya dawo a wannan kakar ba. Ga maganar tashi nan cikin harshen Ingilishi👇👇👇

"Barça and Messi have to be together again one day. This is clear", tells RAC1. 🚨🔵🔴🇦🇷 #FCB


"Maybe could be after his professional career... but Barça and Messi need one last hug, one last dance together".

Tushen Labari: Fabrizio Romano.

A baya-bayan nan dai Messi din ya ki karbar tayin da kungiyar Inter Miami suka yi mishi.

Lionel Messi

KALLI WASANNIN WORLD CUP KAI TSAYE

Turawa abokan ka ta kafafen sadarwa 👇👇👇