Wata Mata ta binne Jaririnta da ran sa a Jigawa.
An kama, wata Mata, mai shekaru 30 a duniya, Balaraba Shehu, da ke ƙauyen Tsurma, na ƙaramar hukumar Kyawa, a jihar Jigawa, bisa zarginta da laifin binne jaririyarta, a cikin banɗaki.
Da ya ke tabbatar da kama matar, Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ta Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana cewar, tunda da farko rundunar ta su ta samu rahotan afkuwar hakan ne, inda kuma cikin hanzari ta Aike da tawagar Jami'an tsaro ƙauyen da ake zargin lamarin ya auku.
Da zuwan Jami'an ne kuma sai su ka tarar an haƙo jaririyar da matar ta binne, a cikin bayan gida.
Tuni dai, Jami'an ƴan sanda, su ka cika hannun su, da wannan mata mai katoɓara, dan zurfafa bincike, da kuma girbar abin da ta shuka.
Matar ta bayyanawa rundunar yan sanda cewa ta binne jaririn ne saboda ba da aure ta haife shi ba, ta bayyana cewa wani tsohon saurayin ta mai shekaru 25 shine yayi mata cikin.
Tawagar yan sanda ta hanzarta ɗaukar jaririn, tare da miƙa shi ga babban Asibitin birnin Dutse, ya yin da Likita ya tabbatar da cewa ya riga mu gidan gaskiya.
Tushen Labari: BBC HAUSA
Turawa abokan ka wannan labari 👇👇👇


0 Comments