Gwarzon dan wasan Argentina kuma dan wasan kungiyar Paris Saint Germain (PSG) Lionel Messi ya sake kafa tarihi guda biyu a yau din nan Asabar 3-12-2022. 

A wasan daya buga yau, tsohon dan wasan Barcelonan, kuma jagoran 'yan wasan Argentina din ya kafa tarihi kamar haka: 


Lionel Messi

TARIHIN DA MESSI YA KAFA

  • Messi ya buga wasan sa na 1,000 a duniya a yau din nan Asabar 3-12-2022.
  • Sannan a karon farko ya ci kwallo ta farko a gasar cin kofin duniya a zagayen da ba na rukuni ba.


Wato Messi din bai taba ciwa Argentina kwallo a rukunin zagaye na 16 ba ko kuma Quarter Final ko Semi Final. Hakan kuwa babban tarihi je gare shi.


A wani bangaren kuma, abokin hamayyar dan wasan wato Christiano Ronaldo shima bai taba cin kwallo a zagayen da ba na rukuni ba. Misali, Ronaldo bai taba cin kwallo ga Portugal a zagaye na 16 ko Quater Final ba.

Lionel Messi


Ku cigaba da bibiyar fikiramedia.blogspot.com domin samun wasu labaran na wasanni.