Ticker

6/recent/ticker-posts

ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI

 AZUMI (02)



Daga Hadiminku mai neman kyawawan addu'o'inku Sayyid Nuru Daruth-thaÆ™alaini. 


*ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI*


1,2- Ci da Sha duk ɗaya ne wanda aka sani ne kamar Gurasa da Ruwa, ko waninsa kamar ƙasa da Lamurjen bishiya, koda kuwa kaɗan ne sosai.

Abin la'akari kawai shine ya tabbata Abin Ci ne da abin Sha a al'adance ko da ta hanyar hanci ne. 

3- Saduwa/Jima'i namiji ne wanda aka kwanta dashi ko Mace ne, mutum ne ko dabba, ta Gaba ne ko ta dubura, mai Rai ne ko matacce, aikata hakan cikin ganganci - cikin niyya da sani - yana karya azumi koda ba a yi inzali  ba - fitar da maniyyi shine inzali. 

4- inzalin maniyyi ta hanyar istimna'i ko Shafefeniya - Shafa ko Shafi na Shafa - da makamancin hakan.

5- Gangancin wayar gari cikin Janaba har alfijir ya fito a watan Ramadhan da Ramuwarsa. 


Baya inganta ramuwar azumin watan Ramadhan daga wanda ya wayi gari da Janaba. 


Wanda yayi janaba a watan Ramadhan ya halasta yayi bacci kafin wanka idan zai iya tashi koda bayan farga ko farga na biyu ya kuma komawa kai sama da sau biyu ma musamman tare da sanin zai tashin. 


Da mai janaba zai bacci tare da yiwuwar zai iya tashi kuma bai tashin ba har alfijir ya fito to akwai fuskoki biyu akansa:


a- Idan yayi gini akan zai tashi yayi wankan kafin alfijir É—in, to babu komai akansa. 


b- Idan bai yi gini akan haka ba hukuncin zamowa a cikin Janaba da gangan na kansa, duk É—ayane yayi gini akan rashin wankan idan ya tashi ko kuma yana kaikawo a ciki, ko kuma bai yi niyyar ba, to idan bai kasance mai kaikawo ba. 


6- Gangancin yin ƙarya ga Allah da Manzonsa (S) da

Imamai (A), kuma IhtiyaÉ—i na Wajibi haÉ—awa har da sauran Annabawa da Wasiyyai (A). 


7- Dulmiya kai a cikin ruwa - muÉ—laÆ™i - abisa ihtiyaÉ—i na Wajibi koda kuwa an fitar da jikin waje. 


8- Isar da ƙura mai kauri cikin maƙogaro.


Ƙura mai kaurin da bata ɓata azumin ta haɗa da:

a- ƙurar da ba mai kauri ba.

b- Turiri sai dai idan ya canja a baki ya zama ruwa aka haÉ—iye. 

c- HayaÆ™i, kuma IhtiyaÉ—i na Wajibi haÉ—awa da Shan Taba. 


9- Allura da abin ruwa, amman babu laifi da daskararren abu. 


10- Gangancin Amai koda da lalura ne. 


Dukkanin abinda ya gabata banda zamowa a cikin Janaba yana ɓata azumi idan ya afku da ganganci ba da waninsa ba, kamar mantuwa. Kuma ganganci yana ɓatawa ba tare da bambamci ba tsakanin Masanin Hukuncin da Jahiltarsa, idan ya kasance Muƙassar ne kai abisa ihtiyaɗi na wajibi koda ya kasance ƙaasir.


i) Aikin jahilin da yake muƙassari wanda yake da lura ba tare da taƙalidi ba ɓatacce ne, sai dai idan yayi shi ne don riskar tabbataccen abu, kuma aka yi sa'a yayi dai-dai da aikin nasa ko da fatawar wanda ya halasta yayi taƙalidin da shi - ma'anar jahili "ƙaasir" shine jahilin da ya zama jahili bisa uzuri kamar gafala, ko yayi kuskure a ijtihadi ko a taƙalidi. wanda ya zama jahili ta sababin sabgogin da ba su bar shi ya san hukunci ba, ko kuma wataƙila baya ganin kansa jahili.



ii) Aikin jahilin da yake Æ™asir ko MuÆ™assarin da yake gafalalle tare da haÆ™iÆ™ance Æ™udurin kusanci ya inganta idan ya kasance yayi dai-dai da tabbataccen abu ko kuma dai-dai da fatawar Mujtahidin da ya halasta ayi taÆ™alidi da shi – Ma'anar Jahili MuÆ™assari shine; Jahilin da yake da damar sanin hukunce-hukuncen da suka hau kansa sai dai kuma yayi gangancin zama a cikin jahilcinsa..


Wallahul-aalim.

Post a Comment

0 Comments