Ticker

6/recent/ticker-posts

SHIN DA GASKE ZA'A KATSE NETWORK RANAR ZABE?

 SHIN DA GASKE ZA'A KATSE NETWORK RANAR ZABE?


Labarin da yake yawo a kafafen sadarwa da kuma guraren zaman jama'a a 'yan kwanakin nan yana cewa ZA'A KATSE NETWORK A RANAR ZABE, shin haka ne?



Kamar yadda kuka sani hukuma ko kuma Gwamnati tana da ikon katse network a ko ina ne a kasar nan. Mun ga irin haka a wasu jihohi da matsalar tsaro ta dama a baya. Kamar Katsina, Zamfara, Borno, Yobe, da sauran su.


Abinda ya kamata ku fahimta shine, shin kun taba jin labarin a gidan Rediyo ko kuma Talbijin ko kuma jarida? Haka kuma ka taba ganin labarin a shafin INEC? 


Idan baka taba jin wannan labarin a gurin su ba to sai kayi watsi da labarin. 



A takaice dai har zuwa yanzu babu labarin da ya sanar da hakan. 


Tabbas za'a iya dakatar da network din wani guri wanda wata matsala kamar ta tsaro ta haddasa, amma ba zai yiwu ace anyi hakan a fadin kasa baki daya ba.


INA TABBATAR MUKU BA ZAI YIWU AYI ZABE BABU NETWORK BA.


Daga karshe, maganar katse network a fadin Najeriya ranar zabe KARYA NE.

Post a Comment

0 Comments