Ticker

6/recent/ticker-posts

TARIHIN SIYASAR MALAM AMINU KANO

 MARIGAYI MALAM AMINU KANO

       (9/8/1920-17/4/1983)


Anhaifi malam Aminu kano a ranar 9-8-1920 a Unguwar Sudawa cikin birnin kano.


Marigayi malam Aminu kano yayi karatun Alqur'ani mai tsarki awajen shehun Malami, Malam Halilu, Malam halilu shine limamin sarkin kano ABDULLAHI BAYERO a shekarar 1929 zuwa 1953.



An sa Malam Aminu Kano a makarantar Primary ta SHAHUCI dake kano a shekarar 1930 lokacin yana dan shekara goma da haihuwa.


Ya zama dalibin kwalejin Kaduna wadda aka samar da ita a 1922 da sunan kwalejin Katsina a katsina daga 1937 zuwa 1942.


Bayan ya gama kwalejin Kaduna ne, Malam Aminu Kano ya samu aikin koyarwa a makarantar Middle School dake Bauchi, inda alokacin Sir Abubakar tafawa balewa yake amatsayin Headmaster.


Daga Bauchi middle school sai aka canzawa Malam Aminu Kano wajen aiki zuwa kwalejin horar da malamai ta Maru dake gundumar sokoto amatsayin headmaster a shekarar 1949 inda yai shekara daya anan kafin daga nan ya ajiye harkar aiki yakama haskokin siyasa gadan - gadan.


Malam Aminu Kano yafara sansanar harkokin siyasa ne tun a shekarar 1943 lokacin daya taimakawa Malam Sa'adu Zungur suka kafa wata kungiyar siyasa mai suna kungiyar cigaban bauchi a jahar bauchi a shekarar 1946.


Malam Aminu Kano da Malam Sa'adu zungur sune suka karfafa kafuwar jam'iyar NEPA wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE ASSOCIATION kafin daga baya takoma NEPU wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE UNION, ankafa jam'iyar ne a shekarar 8 ga watan 8 a shekarar 1950 kuma da mutane 8 aka kafa jam'iyar.


A shekarar 1947 ne Malam Aminu Kano ya jagoranci bude wata kungiya ta malaman arewacin nigeria, kuma dashi aka bude jam'iyar mutanen arewa wadda daga baya tarikede takoma LPC a shekarar 1949 amatsayin jam'iyar dake taimaka mutanen Arewa.



Malam Aminu kano ya rungumi harkokin siyasa sosai wanda har hakan tasa ya ajiye aikinsa a ranar 4 ga watan Nuwamba a shekara 1950.


Malam Aminu Kano yazama shugaban jam'iyar NEPU ta kasa a shekarar 1953 har zuwa lokacin da akayi juyin mulki na farko a nigeria.


Mallam Aminu Kano Yataba cin zabe inda yazama dan majalisar tarayya a shekarar 1959 zuwa 1966 inda ya wakilci Kano ta gabas akarkashin jam'iyar NEPU, shine me tsawatarwa a majalisar hadin gwiwwa.


Mallam Aminu Kano yarike kwamishan lafiya na tarayya kuma dan majalisar zartarwa na koli a gwamnatin tarayya alokacin mulkin Yakubu Gawon.


Malam Aminu Kano dashi akai ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula azamanin Yakubu Gawon wanda Yakubun ya daga bayar da mulkin wanda adalilin hakan ya haddasa hanbarar da gwamnatin ta Gawan din a shekarar 1975 inda Murtala Muhammad ya gaje shi.


Dashi akai gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979.


Malam Aminu Kano shine shugaban jam'iyar PRP kuma dan takararta na shugabancin kasa a shekarar 1979.


Allah yadauki ran Malam Aminu Kano a ranar Asabar 17 ga watan April a shekarar 1983, atsawon shekarunsa na 63 ya shafe shekaru 40 yana gwagwarmayar siyasa dan Talakan Arewa.


Yayi kaurin suna wajen kin manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwadayi kuma baya siyasar kudi face akida zalla kawai.


Indai ka jiyoshi to akan Arewa ne, duk kungiyoyin da yayi ko ya jagoranta to gabadayansu zakuji na AREWA ne.


Bayan mutuwar marigayi Mallam Aminu Kano ansawa muhimman wurare sunansa kamar irinsu filin jirgin sama na kano wato Malam Aminu Kano International Airport da kuma Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano wato Aminu Kano Teaching Hospital.


Allah yajikan Mallam Aminu Kano, Ya Allah kasa matasan Arewa suyi koyi da irin halayyar wadannan bayin Allah nagari, wanda komai nasu akan arewa ne, basu da wayo sai sunji za'a illata AREWA!


© Al'azmiyyah Islamic Foundation

Post a Comment

0 Comments