Kasar Qatar, kuma mai masaukin baki a gasar cin kofin duniya da ake bugawa ita ce kasar da aka fara kora a wannan gasar ta bana.


Qatar din tayi rashin nasara ne har sau biyu a jere cikin wasanni uku da zata buga, hakan na nufin cewa koda Qatar din sun yi nasara a wasa na gaba ba zasu cigaba da buga kofin World Cup din ba. 



Wannan dai shine tarihi mafi muni na kasashen da suke karbar gasar kuma aka kori Qatar din da gaggawar da ba'a taba korar wata kasa a irin wannan karamin lokacin ba.


A wasan ta na farko, Qatar din tayi rashin nasara ne da ci  2-0 a hannun kasar Ecuador, indai a yau kuma tayi rashin nasara da ci 3-1 a hannun kasar Senegal.

World Cup 2022 table for Group A


Fikira Media