𝗦𝗛𝗜𝗡 𝗭𝗔'𝗔 𝗜𝗬𝗔 𝗔𝗠𝗙𝗔𝗡𝗜 𝗗𝗔 (𝗕𝗩𝗡) 𝗗𝗜𝗡𝗔 𝗔 𝗦𝗔𝗧𝗔𝗥 MIN 𝗞𝗨𝗗𝗜 𝗔 𝗕𝗔𝗡𝗞𝗜𝗡𝗔??
Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko
ma'aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin BVN din sa.
Kafin mu bayar da wannan amsar, da farko dai ya kamata mu fara tambayar kanmu shin wai mene ne BVN?
BVN na nufin (Bank Verification Number)
Wato wadansu lambobine da banki suke baiwa kowane mutum bayan sun karbi wadansu bayanai daga gare ka wanda ya kun shi, cikakken sunanka, da adireshinka, da lambar wayarka da hoton fuskarka, da hotunan yan yatsunka.
Wannan shine BVN kuma makasudin yin sa shine domin tabbatar da tsare dukiyar jama'a da tantance adadin jama'ar da suke yin mu'amala da bankuna a kowace kasa.
Bayan banki sun karbi wannan bayanai duk
wani asusun ajiyar kudi da zaka bude a kowane banki ba sai ka sake bayar da bayanan ka ba, kana basu wannan lambar shike nan suna da komai naka.
Sai mu koma ga amsar tambayar mu na cewar Shin ana iya satar kudin mutum ta amfani da BVN?
Wannan maganar kwata-kwata ba gaskiya bace, babu alaka da tsakanin BVN da Account number din ka ta wurin cire kudi. Domin da za ka je banki cire kudi sai ka manta ka rubuta BVN dinka a takardar karbar kudi, mai biya ba zai iya sanina account din ka ba.
Akwai banbanci tsakanin BVN da PIN number dake jikin ATM dinka, wanda shi PIN din ATM shike da hatsari sosai wurin fadawa hannun miyagun mutane.
Yana da kyau ka kiyaye bayyana ATM number din ka, CVV da da ranar da ATM din ka zai expire harma da PIN number din ka.
Yana da hadari ka ringa bayyana PayID din ka domin ana iya satar kudi dashi.
Amma duk da haka ba mu ce ko ina ka saka
BVN dinka ba.
𝗞𝗨𝗬𝗜 𝗦𝗛𝗔𝗥𝗘 𝗗𝗢𝗠𝗜𝗡 𝗬𝗔𝗡 𝗨𝗪𝗔 𝗦𝗨 𝗔𝗠𝗙𝗔𝗡𝗔.


0 Comments