MU KOYI CRYPTO wata manhaja ce da Jabeer Adam Kantama, CEO na Fikira Technologies ya kirkira domin Hausawa masu son koyon Crypto daga tushe.
![]() |
| Mu Koyi Crypto App |
Wannan manhaja tayi bayani na yadda mutum zai fara Crypto tun daga farko har zuwa mataki matsakaici (intermediate).
Shawara: Ka karanta yadda ake dakko App din kafin ka dakko shi. 🙏
Kadan daga cikin abubuwan da Mu Koyi Crypto App ya kunsa:
- Gabatarwa
- Menene Crypto?
- Menene Blockchain?
- Rabe-raben kasuwancin Cryptocurrency.
- Matakin farko na fara Crypto.
- Yadda ake amfani da Bundle Africa.
- Yadda ake amfani da Binance.
- Yadda ake amfani da Kucoin.
- Yadda ake amfani da Trust Wallet.
- Yadda ake amfani da LBank.
- Yadda ake amfani da Hotbit.
- Menene Mining?
- Menene Airdrop?
- Muhimman kalmomi 50 da ya kamata ka sani game da Crypto.
- Menene NFT?
- Menene Metaverse?
- Yadda ake Stacking.
- Menene Futures Trading, ta Yaya ake yin Futures Trading?
- Menene Leverage Trading, ta Yaya ake Leverage Trading?
- Menene Launchpad?
- Menene Launchpool?
- Menene Arbitrage Trading?
- Menene Technical Analysis?
- Yadda zaka Sami Ninki 10 na Kudin ka a Crypto.
- Menene Bot Trading?
- Yadda ake Kasuwancin Data.
![]() |
| Mu Koyi Crypto |
Ta Yaya zaka Sami App din Mu Koyi Crypto?
Kamar yadda kuka sani mafi yawancin Apps ana samun su ne a Play Store ko kuma App Store, to àmma wannan App din bai sami shiga daya daga cikin wadannan manhajoji ba.
Hanya daya muke da ita ta mallakar wannan App, itace kamar haka:
Mun bude wani shafi a Telegram, kayi kokari ka bude shi ta wannan link din:
Bamu saka komai a wannan shafi ba sai App din kawai, ka latsa join sannan ka dakko App din.
Idan ka shiga shafin ka ga sakwannin da yawa, sai ka duba PINNED MESSAGES domin ka lalubo shi.
K tabbata ka yi join din channel din Telegram din domin zamu ringa kawo muhimman abubuwa na Crypto da Fasahar Zamani insha Allah.
Jabeer Adam Kantama


0 Comments