A kullum zaka iya samun free call a layin Airtel idan ka saka shi a irin tsarin da nawa layin yake. A layi na, ina iya samun free call kamar na sakanni 1,000 kowacce rana.
A wannan yanayin da ake ciki, mutane suna bukatar free call, hakan ne yasa nayi wannan rubutun domin ilmantarwa. Amma muna kiran masu karantawa da cewa dan Allah a daure a yada wannan rubutun ga sauran al'umma domin zasu amfana. 🙏
Kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa, wannan wani free call ne dana samu a wani lokaci 👇👇👇
Bayan samun free call, wannan tsarin zai baka damar yin kira mai matukar sauki da rahusa.
- Abin Lura: Wannan tsarin basa bada bonus ko data.
Ta Yaya Ake Shiga Tsarin Free Call din?
Wannan tsarin dai yana aiki ne a layin Airtel kadai.
Domin shiga sai ka kalli wannan bidiyon ko kuma ka cigaba da karantawa. 👇👇👇
- Wannan tsarin sunan sa Freedom, ga yadda ake shiga nan:
- Ka kirawo lambobin *121# a layin ka na Airtel.
- Sai ka danna lamba 5 domin zabar BILLING AND TARIFF.
- Sai ka zabi lamba 3 wanda aka rubuta FREEDOM.
- Zasu ce ka danna lamba 1 domin tabbatar da hakan, sai ka danna.
- Idan kuma kaso zaka iya danna *152# domin shiga tsarin Airtel Freedom din kai tsaye.
Abin Lura: A lokacin da ka shiga ba zasu baka Free Call din ba sai daga baya zasu fara baka. 👌
Muna fatan kun ji dadin wannan mukala sannan zaku turawa yan uwa domin su amfana. 🙏
Jabeer Adam Kantama,
CEO, Fikira Technologies

0 Comments